IQNA

23:33 - September 04, 2019
Lambar Labari: 3484017
Bangaren kasa da kasa, yahudawan Isra'ila sun rusa wani masallaci a garin Khalil da wani gida na falastinawa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa sojojin yahudawan Isra’ila sun kai farmaki kan wani masallaci da ake ginawa a garin Alkhalil dake kudancin gabar yamma da kogin jodan.

A safiyar ranar Litinin motocin Bulldoza na yahudawa sun farwa wani masallaci da ake ginawa a yankin Jabali-Jahoor dake garin Alkhalil tare da rusa shi.

Yahudawa sun yi da'awar cewa ana gina masallacin ne a yankin dake karkashin ikon haramtacviyar kasar Isra'ila.

A cikin wannan shekara, sahayuna sun kara fadada shirinsu na rusa gine-gine da gidajen Palastinawa,domin fadada gine-ginen yahudawa, gwamnatin Isra'ila har wurare masu tsarki ma bata bari ba.

 

3839490

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، khalil ، yahudawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: