IQNA

23:57 - September 10, 2019
Lambar Labari: 3484038
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron Najeriya sun yi amfani da karfi domin tarwatsa masu tarukan ashura.

Kamfanin dillancin labaran iqna, rahotanni daga Najeriya sun tabbatar da cewa jami’an ‘yan sanda sun amfani da karfi domin tarwatsa mambobin Harkar Musulunci da suke gudanar da jerin gwanon ashura a birane daban-daban.

Rahotannin sun ce ‘yan sanda sun yi amfani da harsasan bindiga, inda suka kashe mutane 3 a garin Kaduna tare da jikkata wasu.

Haka nan kuma sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye a wasu garuruwan domin tarwatsawa mabiya Harkar musulunci da suke gudanar da jerin gwanon Ashura, yayin da kuma a wasu biranan an yi tarukan lami lafiya ba tare da jami’an tsaro sun taba wani ba.

 

3841339

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: