IQNA

23:03 - September 12, 2019
Lambar Labari: 3484044
Trump ya yi barazanar cewa, kungiyar Taliban za ta fuskanci munanan hare-hare daga sojojin Amurka.

kamfanin dillancin labaran iqna, a lokacin da yake gabatar da jawabi domin tuanawa da zagayowar ranar 11 ga watan Satumba, wato ranar da aka kai hare-hare kan kasar Amurka, Trump ya yi barazanar cewa kungiyar Taliban ta saurari hare-haren Amurka  da ba ta taba ganin irin su ba.

Ya ce a  cikin ‘yan kwanakin da suka gabata sun gudanar da tattaunawa tare da wakilan kungiyar Taliban, amma wannan tattaunawa ba ta da wani amfani, domin kuwa Taliban ba daina aikin ta’addanci ba.

Trump ya ce; idan Taliban tana tunanin sake zuwa Amurka, to Amurka za ta bi sawunsu a duk inda suke  a duniya, kuma martanin Amurka a akan su ba zai taba zama irin na baya ba.

A cikin wanann mako ne Trump ya sanar da cewa ya soke duk wata tattaunawa da kungiyar Taliban, sakamakon wasu hare-hare da kungiyar ta kaddamar kan sojojin Amurka da ke Afghanistan, inda suka halaka sojin Amurka guda.

3841686

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، donald trump ، Amurka ، Taliban ، Afghanistan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: