IQNA

22:55 - September 25, 2019
Lambar Labari: 3484086
Bangaren kasa da kasa, adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa a Kashmir ta Pakistan ya karu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a Pakistan wata girgizar kasa data abkawa kasar ta yi sanadin mutuwar mutane ashirin da hudu 24 da kuma haddasa barna mai yawa.

Ko baya ga hakan hukumomin kasar sun ce akwai daruruwan mutane da suka raunana ta hanyar karaya da kuma raunuka ka, a girgizar kasar mai karfin maki biyar ad digo biyu a ma’aunin girgizar kasa.

Jami’an agaji sun kwashe daren jiya suna aiki ceto, a yayin da ake garzayawa da wadanda suka raunana a asibitin yankin.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin hanyoyi da gadoji da gidaje da dama sun lalace, ruwan sama da ake samu a yankin na iya kawo cikas wajen gudanar da ayyukan ceto.

 

3844828

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Kashmir ، Pakistan ، adadi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: