IQNA

22:57 - October 24, 2019
Lambar Labari: 3484186
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da mutanen Lebanon ke neman hakkokinsu sunan Muhammad Bin Salman ya bayyana a cikin gangamin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin rahoton da CNN Arabic ta bayar, bayan kwanaki 8 mutanen Lebanon na gangamin neman yaki da rashawa a kasar, sunan Muhammad Bin Salman ya bayyana a cikin gangaminna mutanen Lebanon.

Tashar CNN ta ce dukkanin kafofin da masarautar Al Saud take daukar nauyinsu sun mayar da hankali kaco kaf kan gangamin al’ummar Lebanon tare da kara tunzura su da su yi wa gwamanti bore.

Rahoton ya ce wasu daga cikin tashoshin a cikin Lebanon suna cewa, ya kamata masu gangami su yi aiki da nasihar Bin Salman wajen ci gaba da jajircewa domin neman hakkokinsu.

Wasu daga cikin masu sharhi a tashoshin suna yin izgili ga Sayyid Hassan Nasrullah, wanda ya nuna goyon bayansu ga masu gangamin, amma kuma ya kiraye da su hattara domin kada a yi amfani da su domin a cimma wani burin a daban domin rusa kasar.

 

3852226

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: