IQNA

Aoun Ya Amince Da Murabus Din Hariri A Matsayin Firayi Minista

23:55 - October 31, 2019
Lambar Labari: 3484210
Shugaban kasar Lebanon ya amince da murabus din fira ministan kasar, amma ya bukaci ya ci gaba da rike gwamnati na wucin gadi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Ofishin shugaban kasar Labanon Marsh1l Aun ya fitar da wata sanarwa dake nuna cewa bisa la’akari da ayar doka ta 69 ta kundin tsarin mulkin kasargame da batun da ya shafi murabus din fira minista, a sakin layi na daya ya nuna cewa bayan murabus din Sa’ad Hariri fira ministan kasar, shugaban kasar ya mika godiyarsa game da rawar da gwamnatin Hariri da ministocinsa suka taka, kana ya bukaci gwamnati da ta ci gaba da ayyukanta kafin fara shirye-shiryen kafa sabuwar gwamnati.

A wata sanarwata daban da fadar shugaban kasa ta fitar ta nuna cewa gobe Alhamis ne shugaban kasar Marshal Aun zai yi wa alummar kasar bayani ta gidan talbijin domin murnar zagayowa cika shekaru 8 da hawa madafun iko, inda ake sa ran zai tabo muhimman baututuwa game da halin da ake ciki a kasar.

Wannan yana zuwa ne bayan da aka kwashe kwanaki 14 ana gudanar da Zanga- zanga a fadin kasar domin nuna adawa da halin matsatsin tattalin arziki da alummar kasar ke ciki, lamarin da ya jawo fira ministan kasar Sa’ad Hariri ya sanar da yin murabus daga mukaminsa bayan da lammura suka ki dawo wa dai-dai duk da sabbin tsare tsaren tattalin arziki da ya gabatar.

 

3853510

 

 

captcha