IQNA

17:18 - November 20, 2019
Lambar Labari: 3484257
Jagoran juyin juya hali a Iran ya ce sun tilasta wa makiyan kasar ja da baya a wasu bangarori kuma za su tilsta su ja da baya a bangaren tattalin arziki.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya jinjinawa al’ummar Iran da jami’an tsaro da su ka tilastawa makiya ja da baya akan batutuwa masu alaka da tsaroda su ka faru a bayan nan.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana haka ne a lokacin da ya keganawa da manyan ‘yan kasuwa da masu masana’antu a jiya Talata a birnin Tehran.

Jagoran juyin musulunci na Iran ya tabo batun rikice-rikicen da su ka faru a cikin Iran a bayan nan, bayan matakin da gwamnati ta dauka na kara kudin man fetur, inda ya kara da cewa; “ Wajibi ne ga abokai da ma makiyanmu su san cewa mun yi nasarar ingiza makiya baya ta fuskokin soja, siyasa da tsaro.”

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya ce; Addinin musulunci ya yarda da kyautata rayuwar al’umma dasamar musu da abubuwan more rayuwa,sannan ya kara da cewa mahangar tsarin musulunci ta tattalin arziki ta sha banban da ta jari-hujja ko gurguzu.

Wani sashe na jawabin jagoran juyin musulunci ya yi jinjina ga wadanda su ka fito da hanyoyin kaucewa tasirin takunkumin Amurka, tare da yin kira da a kara daukar matakan kare tattalin arzikin kasa daga duk wani takunkumi anan gaba.

 

3858253

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: