IQNA

17:26 - November 20, 2019
Lambar Labari: 3484259
Dakarun kasar Syria sun harbor wasu makamai masu linzami na Isra’ila a kan birnin Damascus.

Kamfanin dillancin labaran IQNA,  a safiyar jiya ne sojojin kasar Siriya suka kakkabo wasu makamai masu linzami wadanda haramtacciyar kasar Isra’ila ta cillasu kusa da tashar jiragen sama na birnin Damascus babbab birnin kasar.

Kamfanin dillancin labaran SANA na gwamnatin kasar Siriya ya bada labarin cewa an ji karar facewa har sau 4 a kusa da tashar jiragen saman a safiyar yau Talata.

Har’ila yau wata majiyar Haramtacciyar kasar Isra’ila ta bada sanarwan cewa an ji karar jiniya, gargadi a yankin tuddan Golan wanda ke cikin yankunan da haramtacciyar kasar Isra’ila take mamaye da su.

Banda haka wasu labaran sun bayyana cewa sun cilla wasu makamai masu linzamin zuwa yankunan mai kusuruwowi ukku na kasashen Lebanon, Siriya da kuma tuddan Golan da aka mamaye.

 

3858276

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: