IQNA

23:39 - December 06, 2019
Lambar Labari: 3484296
Bangaren kasa da kasa, Firayi inistan Sudan ya bayyana cewa zai fitar da sojojin kasa daga kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga mujallar midleast eye cewa, Abdullah Hamduk Firayi inistan Sudan ya bayyana cewa zai fitar da sojojin kasa daga kasar Yemen a yakin da suke yi a kasar.

Ya bayyana hakan ne yau a wajen taron majaisar Atlantic a birnin Washington, inda ya bayyana cewa kasarsa ta gaji wani yaki da Umar Albashir ya jefa kasar a Yemen.

Hamdu ya ce babu wani daily da zai sanya kasar Sudan ta shiga yaki da Yemen, domin kuwa ‘yan uwansu musulmi da larabawa ne kawai ae kashewa a wannan yaki, wanda hakan bai dace ba.

Tun a cikin sekara ta 2015 ce dai Umar Hassan Albashir ya shigar da sojojin Sudan cikin yakin da Saudiyya ta kaddamar kan al’ummar kasar, inda suke yin yaki a matsayin sojojin hayar Saudiyya.

3862043

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3862043

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Sudan ، Yemen ، dakaru
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: