IQNA

14:13 - December 11, 2019
Lambar Labari: 3484309
Bangaren kasa da kasa, an gayyaci limamin wani masallaci da ya fassara ayoyin kur’ani bisa kure a Masar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na sadal balad ya habarta cewa, Sabri Ibadah mataimain ministan harkokin addini ya bayyana cewa a jiya an gayyaci limamin wani masallaci da ya fassara ayoyin kur’ani bisa kure a Masar a garin Tanta da ke cikin lardin Garbiyya a kasar.

Wannan mataki dai yana zuwa ne bayan da limamin ya fassara wasu ayoyin kur’ani a cikin hudubar juma’a bisa kure, wanda hakan ya dauki hankulan jama’a.

An nada wannan limami ne dai tun a kimanin shekaru ashirin da suka gabata, inda kuma yake gabar da huduba a kowace Juma’a, wanda hakan yasa cibiyar azhar ta nuna takaicinta da faruwar hakan.

 

https://iqna.ir/fa/news/3863034

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Masar ، limami ، kure
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: