IQNA

23:56 - January 12, 2020
Lambar Labari: 3484407
Musulmin kasar Uganda sun sanar a cikin wani bayani cewa, kisan Kasim Sulaimani abin yin tir da Allawadai ne.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Sheikh Isma’il Du’a, shugaban majalisar musulmin kasar Uganda ya aike da wata wasika zuwa ga jakadan kasar Iran a Uganda da ke birnin kampala, inda a cikin wasikar ya isar da sakon ta’aziyyar shahadar janar Kasim Sulaimani.

A cikin matanin wasikar malamin ya ci gaba da cewa; kisan gillar da aka yi Kasim Sulaimani lamari ne da ya shafi dukkanin musulmi baki daya, domin kuwa shi mutum ne da ya kasance a  sahun gaba wajen kare martabar addinin muslunci.

Haka nan kuma malamin ya ce a madadin dukaknin musulmin kasar Uganda, suna kara jaddada kira kan wajabcin hadin kan al’ummar msuulmi, domin hakan shi ne a cewarsa shi ne kadai mafita guda da ta rage ga msuulmi a halin yanzu.

A cikin wanann mako majalisar musulmin kasar ta Uganda ta aike da sako ga dukkanin liammai na jihohi 8 a kasar, kan su yi Allawadai da kisan Kasim Sulaimania  cikin hudubobin Juma’a.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3871044

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: