IQNA

18:51 - January 17, 2020
Lambar Labari: 3484425
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa sojojinta 11 sun jikkata a harin ramuwar gayya da Iran ta kai mata.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, mai Magana da yawun cibiyar kula da ayyukan rundunar sojojin Amurka CENTCOM ya bayyana cewa, sojojin Amurka 11 ne suka samu raunuka sakamakon hare-haren da Iran ta kaddamar a kan sansanin sojin Amurka a Iraki.

Ya ce an dauki 8 daga cikin dakarun da suka samu raunuka zuwa kasar Jamus domin yi musu magani, yayin da 3 daga cikinsu suna nan a asisbitin sansanin sojin Amurka na Arifjan da ke Kuwait ana kula da su.

Kakakin ma’aikatar tsarin kasar Amurka ta Pentagon ya bayyana cewa, bayan da sakataren tsaron kasar ta Amurka ya samu bayani kan adadin sojojin Amurka da suka jikkata a wannan hari, ya bayar da umarnin kai asibitotin na Jamus da kuma Kuwait domin samun kula.

Harin martanin na Iran kan sansanin sojin na Amurka da Ainul Asada a Iraki, ya yi sanadiyyar rusa wasu daga cikin manyan kayan yakin Amurka da suka hada hard a jirage masu saukar angulu na yaki.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3872174

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، kula ، tsaron kasa ، Amurka ، Iran
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: