IQNA

Tsohuwar Minista A Faransa Ta Bukaci A Rika Koyar Da Kur’ani A Makarantu

22:18 - January 18, 2020
Lambar Labari: 3484428
Najat Falu Bilqasim tsohuwar ministar ilimi mai zurfi a kasar Faransa ta bukaci da a rika koya kur’ania  makarantu.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na sabaq ya bayar da rahoton cewa, Najat Falu Bilqasim tsohuwar ministar ilimi mai zurfi a kasar Faransa, wadda ‘yar asalin kasar Morocco ce, ta bayyana cewa koyar da kur’ani a makarantu a Faransa ya zama wajibi.

Tsohuwar ministar ta bayyana hakan nea  wata zantawa da tashar RTL ta kasar faransa, inda ta ce kyamar addinin musulunci na karuwa cikin sauri a  Faransa.

Bilaqsim ta ce wannan na faruwa ne sakamakon rashin masaniya kan addinin muslunci a tsakanin mtanen kasar Faransa, kamar yadda ta bayyana saka hijabi a matsayin ‘yanci ne na addini.

Ta ce koyar da kur’ani zai taimaka wajen rage kyamar addinin muslunci a kasar, kamar yadda kuma ta bukaci da a janye dokar hana mata saka hijabia  wuraren ayyuka ko makarantu.

 

https://iqna.ir/fa/news/3872278

captcha