Majiyar ta ce matakin na Saudiyya na tsagaita wutar yaki wacce za ta fara daga yau Alhamis, ya zo ne saboda kokarin hana yaduwar cutar Corona da ta zama annoba a duniya,kamar yadda su ka ambata.
Jami’an sojan kawancen na Saudiyya suna bayyana fatansu na cewa Kungiyar Ansarullah ta Yemen wacce aka fi sani da ‘yan huthi za su amince da matakin.
Jami’in ya kuma kara da cewa Abu ne mai yiyuwa a sake tsawaita lokacin tsagaita wutar.
A gefe daya, mataimakin ministan tsaron Saudiyya Khalid Bin Salman, ya ce; Saudiyyar tana goyon bayan kiran da majalisar dinkin duniya ta yi na ganin an kawo karshen yaki da kuma bude kofar tattaunawa a tsakanin masu fada da juna din a kasar Yemen.
Sai dai a daya bangen gwamnatin San’a tuni ta karyata wannan ikirari na mahukuntan Saudiyya, inda suka ce har zuwa yammacin yau Alhamis, jiragen yakin Saudiyya suna ci gaba da yin luguden wuta a kan yankuna daban-daban na kasar Yemen.