IQNA

Ana Ci Da Yin Tir Da Matakin Trump Na Yanke Tallafi Ga Hukumar WHO

23:56 - April 15, 2020
Lambar Labari: 3484715
Tehran (IQNA) kasashen duniya da bangarori daban-daban suna ci gaba da yin kakkausar suka kan matakain Trump na yanke tallafin Amurka ga hukumar WHO.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, duniya na ci gaba da yin kakkausar dangane da matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na yanke tallafin Amurka ga hukumar lafiya ta duniya, a daidai lokacin da ake fuskantar annobar corona.

Trump ya fake da cewa hukumar ba ta yi aikinta yadda ya kamata ba wajen bayyana wa duniya hadarin corona tun daga farko, wanda a cewarsa hakan ne ya cutar da Amurka a halin yanzu.

Babban sakataren majlaisar dinkin duniya ya mayarwa Trump da martani, inda bayyana cewa wannan ba lokaci ne na yanke tallafi ga hukumar lafiya ta duniya ba.

Ita ma a nata bangaren kungiyar tarayyar turai t abayyana matakin an Trump da cewa abin ban takaici ne, tare da kiransa kan ya sake yin nazari kan wannan mataki domin kuwa ba maslaha ce ga ita kanta Amurka ba.

A nasa bangaren babban kwamishinan kungiyar tarayyar Afrika Musa Muhammad Faki ya bayyana matakin na Trump da cewa bai yi tarayyar Afirka dadi ba.

3891974

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha