IQNA

Shugaba Rauhani:
22:38 - May 20, 2020
Lambar Labari: 3484817
Tehran (IQNA) Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa, Iran za ta ci gaba da kasancewa tare da al’ummar Falastinu har sai sun samu hakkokinsu da aka haramta musu a kasarsu.

A lokacin da yake gabatar da wani jawabi a yau Laraba a taron majalisar ministoci a birnin Tehran, shugaba Rauhani ya bayyana cewa, Iran tana nan kan matsayinta na ci gaba da kasancewa tare da al’ummar Falastinu, har sai sun samu dukkanin hakokinsu da aka haramta musu.

Rauhani ya ce, a kowace shekara ana gudanar da ranar Quds ta duniya domin raya wannan tunani na taimaka ma al’ummar Falastinu, da kuma kubutar da su daga mawuyacin halin da aka jefa su da gangan, domin cimma manufofi na ‘yan mulkin mallaka.

A kan haka Rauhani ya ce za a ci gaba da raya wanann rana, domin hakan shi ne raya ruhin al’ummar Falastinu, kuma ta haka ne za su san cewa al’ummomin duniya masu ‘yancin siyasa da lamiri suna tare da su.

Ya ce al’ummar Falastinu suna ci gaba da kara shiga cikin mawuyacin hali, sakamakon ci gaba da kara mamaye yankunansu tare da mayar da su baki a cikin kasarsu, kuma abin ban takaici hakan yana faruwa ne a idanun dukkanin al’ummomin duniya, adaidai lokacin da masu da’awar kare hakkokin bil adama da Demokradiyya suka yi gum da bakunansu kan hakan, yayin da wasu daga cikinsu ma suna bayar da gudunmawa domin kara danne al’ummar falastinu.

Daga karshe shugaba Rauhani ya yi kira ga al’ummomin duniya, da su sauke nauyin da ya rataya a kansu, wajen taimakon al’ummar falastinu marassa ta dukkanin hanyoyin da suka sawaka.

3900322

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Quds ، masallaci ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: