IQNA

Saukar Kur’ani Mafi Girma Ta Hanyar Yanar Gizo A Indonesia

23:53 - May 27, 2020
Lambar Labari: 3484842
Tehran (IQNA) an gudanar da saukar kur’ani mafi girma ta hanyar yanar gizo a Indonesia wanda jihar Jawa ta dauki nauyinsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Khafifa Indar gwamnan lardin Jawa  kasar Indonesia ce ta jagoranci gudanar da wannan sauka ta hanyar yanar gizo, wadda dubban makaranta da mahardata suka shiga.

An gudanar da wannan sauka ne a daren 27 na watan Ramadan domin samun albarkar lailatul qadri, inda aka yi daruruwan sauka a dare guda ta hanyar yanar gizo, wanda kuma shi ne irinsa na farko a tarihia  duniya.

An baiwa gwamnan jihar jawa ta kasar Indonesia kyauta ta msamman kan wannan saukar kur’ani da ta jagoranta, amma ta bayyana cewa wannan kyat ace ga mahardata fiye da dubu 4 na kasar Indonesia da gwamnoni 17 na jihohin kasar da suka shiga cikin wannan sauka.

Ta ce wannan babban abin farin ciki ne da alfahari ga al’mmar musulmi na kasar Indonesia da ma musulmi na duniya baki daya.

 

3901478

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: indonesia kasar kyauta
captcha