IQNA

An Bude Masallatai A Kasar Tunisia Bayan Rufe Su Na Watanni Uku

23:52 - June 05, 2020
Lambar Labari: 3484865
Tehran (IQNA) an bude masallatan kasar Tunisia domin ci gaba da gudanar da salla bayan rufe su na tsawon watanni uku.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, tun a ranar Laraba da ta gabata ce aka bude dukkanin masallatai a kasar Tunisia domin ci gaba da gudanar da salla bayan rufe su na tsawon watanni uku a jere.

Ministan ma'akatar kula da harkokin addini a kasar ya bayyana cewa, dole ne kowane mutumzai zo masallaci ya zo da dardumarsa domin yin salla.

Haka nan kuma ya jaddada cewa, wajibi ne a kiiyaye dukkanin kaidoji da dokoki da jami'an kiwon lafiya suka kafa domin hana kamuwa ko yaduwar cutarcorona, da hakan yahada da saka takunkumin rufe fuska da wanke hannuwa.

a jiya an bayar da rahoton cewa ba a samu mutum ko daya da ya kamu da cutar corona  a kasar Tunisia ba, inda adadinin wadanda suka kamu baki daya ya kai 1087, sai kuma 968 sun warke 49 kuma sun rasa rayukansu.

 

https://iqna.ir/fa/news/3903028

captcha