IQNA

Fatawar Ayatollah Sistani Ce Ta Fitar da daesh daga Iraki

23:03 - June 13, 2020
Lambar Labari: 3484890
Tehran (IQNA) kungiyar dakarun Nujba ta sanar da cewa, fatawar da Ayatollah Sistani ya bayar da c eta fitar da daesh daga Iraki.

A shafinta na yada labarai, kungiyar Nujba ta sanar da cewa, tun bayan da Ayatollah Sistani ya bayar da fatawa a shekarar 2014 kan wajabcin yakar kungiyar daesh da kare kasar Iraki, daga lokacin ne Daesha ta fara ganin turjiya daga al’ummar kasar.

Bayanin ya ce fatawar ad Ayatolah Sistani ya bayar c eta sanya miliyoyin matasan kasar Iraki shiga cikin kungiyoyin sojojin sa kai, wadanda kuma su ne suka  fitar da Daesh daga Iraki tare da murkushe ta saboda wannan fatawa.

Tun lokacin da kungiyar ‘yan ta’addan wahabiyya na Daesh suka shiga Iraki daga kasashen larabawa da suke daukar nauyinsu.

Haka nan kuma dakarun sa kai na Hashd sha’abi sun taka gagarumar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar Iraki, wanda hakan ne ya kai kasar ga samun zaman lafiya yanzu.

 

3904558

 

captcha