IQNA

Yara Uku Makafi ‘Yan Gida Guda Da Suka Hardace Kur’ani

18:49 - July 14, 2020
Lambar Labari: 3484985
Tehran (IQNA) Hebah, Nurul Huda da Mustafa ‘yan kasar Syria da suke zaune Aintab da ke Turkiya wadanda suka hardace kur’ani mai tsarki.

Shafin yada labarai na Orient-News ya bayar da rahoton cewa, Hebah Alqnawi yar shekaru 18, Nurul Huda shekaru 13, da Mustafa shekaru 11, ‘yan kasar Syria da suke zaune Aintab da ke Turkiya wadanda suka hardace kur’ani mai tsarki wadanda kuma dukkaninsu suna da larurar gani.

Wadannan ‘yan juna su uku dai sun hardace kur’ani ne tare da taimakon mahaifansu da kuma ‘yan uwansu, ta hanyar saka musu karatun kur’ani suuraro kuma suna bi.

Hussain Hazerlar shi ne shugaban cibiyar bayar da fatawa ta yankin Aintab, ya bayyana cewa hakika lamarin wadannan yara yana ban alajabi da kuma burgewa.

Ya ce yadda wadannan yara uku suka hardace kur’ani da kuma yadda hakan ya yi tasiri a rayuwarsu, shi kansa da ya ce daga cikin mu’ujizozin kur’ani mai tsarki.

Mahaifiyar wadannan yara uku ta bayyana cewa, ba ta fuskanci wata matsala wajen koyar da su harder kur’ani ba, duk abin da ta koya musu suna hardacewa  a nan take.

Mustafa wanda shi ne karami daga cikinsu ya bayyana cewa, ya hardace kur’ani baki daya  acikin shekara guda, inda yake yin amfani da hanyar sauraren karatun kur’ani yana bi, yana maimaitawa har ya hardace baki daya.

 

3910415

 

captcha