IQNA

An Kaddamar da Littafi Da Ke Magana Kan Rayuwar Musulmi A Philippines

14:41 - July 22, 2020
Lambar Labari: 3485007
Tehran an kaddamar da wani littafi da yake magana a kan yanayin rayuwar musulmi a kasar Philippines da ma wasu yankunan gabashin asia.

A yayin kaddamar da littafin, karamin jakadan Iran a kasar ta Philippines Muhammad Jaafar Molk, da kuma Tandis Taqavi wadda ta rubuta littafin, sun gabatar da jawabi matsayin rayuwar musulmi a yankin, da kuma banbancinta da sauran yankuna.
A cikin littafin marubuciyar ta yi kokarin bayyana yadda musulmi suke rayuwa a kudancin kasar ta Philippies, wadda mafi yawan mutanen kasar mabiya addinin kirista ne, sai kuma wasu mabiya addinai wadanda su ne marassa rinjaye kamar musulmi da sauransu.

Abu mai ban sha’awa shi ne, yadda musulmin kasar suka kasance masu riko da addininsu, ba tare da tasirantuwa da yanayin zamantakewa ba, duk kuwa da cewa ba su fuskantar wata matsala saboda addininsu daga bangaren mahukunta a matsayinsu na musulmi.
Irin wannan yanayi ya yi kama da sauran yankunan gabashin nahiyar Asia, in banda kasar Burma wadda kyamar musulmi da addinin muslucni aka halasta shi, kuma ya zama wani bangare na dokar gwamnati.
Haka nan kuma marubuciyar ta kwatanta yanayin rayuwar musulmi a kasar ta Philippines da wasu daga cikin kasashen turai, inda take bayyana cewa yayin kama da rayuwar musulmi a wasu kasashe, a wasu kasashen kuma ya sha banban.
A jimlace dai marubuciyar ta bayyana yanayin rayuwar musulmin kasar da cewa rayuwa ce da take misilta zamantakewa da kuma zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin msuulmi da sauran mabiya addinai.

 

3911997

 

Abubuwan Da Ya Shafa: rayuwa ، addinai ، misilta ، mabiya addinai ، musulmi ، philipines
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha