IQNA

23:35 - July 23, 2020
Lambar Labari: 3485010
Tehran (IQNA) babban malamin ahlu sunnah mai bayar da fatawa na Iraki ya ce dole ne a  aiwatar da kudirin da ya bukaci ficewar Amurkawa daga Iraki.

Kamfanin dillacin labaran Awajil News ya bayar da rahoton cewa, Sheikh Mahdi Al-sumaida’i babban malamin ahlu sunnah mai bayar da fatawa na Iraki ya ce; dole ne a  aiwatar da kudirin da majalisar dokokin kasar ta amince da shi wanda ya bukaci ficewar Amurkawa daga Iraki baki daya.

Ya ce duk wani mamba na ahlu sunna da ke cikin majalisar dokokin Iraki da bai goyi bayan ficewar sojojin Amurka daga kasar ba, to baya wakiltar wadanda suka zabe shi.

Kwanaki biyu bayan kisan gillar da Amurkawa suka yi wa Kasim Sulaimani da Abu Mahdi Almuhandis, majalisar dokokin Iraki ta bukaci ficewar sojojin Amurka daga kasar.

 

3912185

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Kasim Sulaimani ، Iraki ، kisan gilla ، ficewar ، amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: