IQNA

Bayanin Kungiyar Hizbullah Kan Abin Da Ya Faru A Beirut

20:03 - August 05, 2020
Lambar Labari: 3485057
Tehran (IQNA) Kungiyar Hizbullah ta fitar da bayani kan hatsarin da ya auku a birnin Beirut wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama.

A cikin bayanin, kungiyar Hizbullah ta bayyana abin da ya faru da cewa babban abin bakin ciki ne ga kasar da kuma al’ummarta, tare da bayyana hakan a matsayin daya daga cikin ibtila’o’in da kasar take fuskanta a halin yanzu.

Bayanin ya ce kungiyar Hizbullah tana taya dukkanin al’ummar Lebanon alhinin abin da ya faru, musamamn ma iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata, gami da wadanda suka yi asarori sakamakon hakan.

Jim kadan bayan faruwar lamarin a  jiya, Isra’ila ta fito ta bayyana cewa ba ta da hannu a cikin abin da ya faru a Beirut.

Wannan lamari dai ya faru ne a daidai lokacin da ake jiran hukuncin kotun majalisar dinkin duniya kan kisan tsohon fira ministan kasar Rafiqul Hariri, wanda aka kashe shi kimanin shekaru 15 da suka gabata, wanda dukkanin alamu kan yadda aka aiwatar da kisan, na nuni ne da irin salon da Isra’ila ta saba bi ne wajen kashe manyan mutane a kasar Lebanon.

Sai dai kotun wadda aka riga aka siyasantar da aikinta, manyan kasashe irin su Amurka da kawayenta gamin da wasu ‘yan korenta daga cikin kasashen larabawa ne suke da tasiri a kanta, wadda tun lokacin da ta fara bincike kan kisan Hariri, babban abin da ake so ta aiwatar a zahiri shi ne, ta dora alhakin hakan a kan kungiyar Hizbullah wadda ta ‘yanto kasar ta Lebanon daga mamayar Isra’ila, wanda kuma ake sa ran sanar da da hukuncin kotun kan kisan Hariri a ranar 7 ga wannan wata na Agusta da muke ciki.

3914741

 

captcha