Shafin yada labarai na Misril yaum ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani sako da suka aikewa ma’aikatar kula da harkokin addini, malamai da limamai a kasar Masar sun yi kira ga gwamnatin kasar kan ta bayar da damar bude cibiyoyi na kur’ani a kasar ta Masar.
A cikin sakon wanda suka aikewa ministan ma’aikatar kula da harkokin addini na kasar Mukhtar Juma’a, malaman sun bukaci a bude cibiyoyin da makarantu, domin ta hanyar hakan za a samu damar ci gaba da bayar da tarbiya ta addini da kuma koyarwar kur’ani a tsakanin matasa.
Daga karshen sakon nasu sun bukaci ministan matsayinsa na malami masanin addini, da ya yi amfani da matsayinsa wajen ganin an cimma wannan buri musamman ganin cewa an dauki lokaci cibiyoyin ilimi suna rufe saboda cutar corona.
3925181