IQNA

Haniyya: Ba Za Mu Bar ‘Yan Uwanmu A Gidajen Kason Yahudawa Ba

22:30 - October 20, 2020
Lambar Labari: 3485293
Tehran (IQNA) jagoran Hamas ya bayyana ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin Falastinawa a matsayin gishikin nasara.

 

 

Shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Falasdinawa Hamas ya bayyana cewa babu wata takurawan da za’a yi Falasdainuwa wanda zai hana su ci gaba da tattaunawa don samun hadin kan mutanensu a cikin kasarsu da aka mamaye da ita.

Isma’ila Haniyyar shugaban kungiyar Hamas yana fadar haka ne a lokacinda yake hira ta kafar bidiyo da jakadan MDD na musamman kan lamuran sulhu a gabas ta tsakiya a jiya Litinin.

Haniya ya kara da cewa babban kungiyar Falasdinawa ta Fatah da kuma ta hamas sun zasu ci gaba da aiki tare don kaiwa ga manufarsu ta hada kan al-ummar Falasdinu a cikin kasar.

Haniya ya jaddada matsayinsu na ci gaba da bin kadun Falastinawa da suke tsarea  gidajen kason yahudawa, inda ya ce ba za su bar ‘yan uwansu da ake tsare da su a wadannan gidajen kurkuku ba.

 

3930303

 

 

 

 

 

captcha