IQNA

23:58 - November 09, 2020
Lambar Labari: 3485350
Tehran (IQNA) an fara gudanar da bincike kan wani hari a aka kai kan wani masallaci a birnin Wagadugu na kasar Burkina Faso.

Kamfanin dillancin labaran Africa CGTN ya bayar da rahoton cewa, wani mutum ne da ba a san kowane ba, ya jefa wani abu mai fashewa a cikin wani masallaci a ranar Juma’a da ta gabata.

Wata mata da ta sheda abin da ya faru, ta tabbatarwa kamfanin dillancin labaran AP cewa, a gaban idonta mutumin ya jefa wani abu mai fashewa a lokacin da musulmi suke ibada a cikin masalaci, kuma lamarin ya yi sanadiyyar jikkatar mutane da dama, da hakan ya hada har da konewar jiki.

Ministan tsaron cikin gida a  kasar Burkina Faso Ousseni Compaore ya ziyarci masallacin domin ganewa idonsa abin da ya faru, inda ya sha alawashin cewa za a gudanar da binike kan wannan lamari, tare da gano duk wadanda suke da hannu a wannan hari domin hukunta su.

Ana danganta wannan harin ne da masu kiyayya da musulmi a kasar, duk kuwa da cewa kasar Burkina Faso kasa ce da musulmi da kiristoci da ma masu bin addinan gargajiya suke zaune lafiya da juna.

A cikin shekarun baya-bayan kasar ta fara fuskantar matsalolin tsaro sakamakon sadadowar da ‘yan ta’adda suke daga kasar Mali suna kaddamar da hare-hare musamman a yankunan arewacin kasar da ke kusa da iyaka da kasar Mali.

 

3934197

Abubuwan Da Ya Shafa: arewacin ، burkina faso ، yankunan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: