IQNA

Sheikhul Azhar Ya Yi Da A Yi Adalci Wajen Raba Rigakafin Corona

22:57 - November 18, 2020
Lambar Labari: 3485377
Tehran (IQNA) babban malamin cibiyar Azhar a kasar Masar ya kirayi manyan kasashen duniya da su yi adalci wajen raba riga kafin corona.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ya fitar kan halin da ake ciki dagane da corona da kuma batun samar da rigakfin wannan cuta, babban malamin na cibiyar Azhar sheikh Ahmad Tayyib ya kirayi manyan kasashen duniya da su yi adalci wajen raba riga kafin da aka samar.

Ya ce a halin aynzu akwai mutanen da suka da bukatar taimakon gagawa wadanda basu da hanyar da za su iya samun wannan rigakafi sai ta hanyar taimakon manyan kasashe.

Ya ce akwai miliyoyin mabukata a duniya da suke fama da talauci wadanda basu da galihu, haka nan kuma akwai dubban daruruwan ‘yan gudun hijira wadanda suke bukatar taimako, dukkanin wadanan bai kamata a manta da su ba.

A cikin wannan makon ne dai wasu daga cikin manyan cibiyoyin bincike na duniya suka sanar da cewa sun samar da maganin rigakafin cutar corona.

 

3935805

 

captcha