IQNA

23:01 - November 18, 2020
Lambar Labari: 3485379
Tehran (IQNA) tawagar gwamnatin kasar Bahrain ta fara gudanar da wata ziyara a hukumance a  Isra’ila.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Bahrain ta bayar da bayanin cewa, wata tawagar gwamnatin kasar karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Abdullatif Bin Rashid Azayani ta isa birnin Tel Aviv na Isra’ila a yau Laraba.

Bayanin ya ce waannan ita ce ziyara ta farkoa  hukumance da tawagar gwamnatin Bahrain ta fara kaiwa a Isra’ila, kuma nan gaba za a ci  gabada ganin irin wannan ziyara tsakanin jami’an gwamnatocin Isra’ila da na Bahrain.

Ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan Isra’ila Gabi Ishkinazi ne dai da kansa ya rabi tawagar ta gwamnatin Bahrain a Telaviv, inda ya bayyana ziyarar tasu da cewa ta tarihi ce a  tsakainsu.

To sai dai a daya bangaren al’ummomin kasar Bahrain suna ta yin tofin Allah tsine dangane da wannan ziyara, inda suke ta yin bayanai a shafukan sadarwa na zumunta, kan cewa wannan ziyara ba da sunansu ake gudanar da ita ba.

Gwamnatin Bahrain ta sanar da kulla alaka tsakaninta da Isra’ila ne tun a cikin watan da ya gabata, amma majiyoyin kafofin yada labaran gwamnatin Isra’ila sun bayyana cewa akwai alaka ta boye tsakanin Israila da Bahrain tun kusan shekaru talatin da suka gabata, a yanzu dai alakar ta fito fili ne a hukumance.

3936057

 

Abubuwan Da Ya Shafa: gwamnatin Bahrain ، tawaga ، hukumance ، kafofin yada labarai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: