IQNA

Kotu Ta Soke Dokar Hana Saka Hijabi A Makantu A Sweden

22:48 - November 19, 2020
Lambar Labari: 3485381
Tehran (IQNA) kotu a yankin Skane na kasar Sweden ta soke dokar hana mata musulmi saka hijabi a makarantu.

Kamfanin dillancin labaran Anadulo ya bayar da rahoton cewa, a jiya kotun yankin Skane na kasar Sweden ta soke dokar hana mata musulmi saka hijabi a makarantu.

Wannan kotu ta dogara ne da dokar da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar ta Sweden wanda ya baiwa kowa dama da ‘yanci na yin addininsa daidai da yadda ya fahimta, ba tare da tauye masa hakkinsa na yin abin da addininsa ya koyar da shi ba.

Wani babban jami’i a ma’aikatar shari’a ta kasar Sweden ne dai ya fara gabatar da wannan batu, inda yake ganin cewa hana mata musulmi saka hijabin muslunci a makarantun kasar ya saba wa doka, a kan haka ya bukaci da a janye wannan doka.

Kamfin wannan lokacin dai an yi ta kai ruwa rana kan yadda wasu suke kallon musulmi a kasar a matsayin barazana, yayin da kuma wasu ke ganin cewa musulmi suna da hakki kamar kowane dan kasa.

3935939

 

 

captcha