IQNA

14:42 - November 21, 2020
Lambar Labari: 3485385
Tehran (IQNA) babban kwamitin musulmin kasar Amurka ya caccaki shugaban kasar Faransa kan matakan takurawa musulmin kasar.

Shafin yada labarai na Middle East Eye ya bayar da rahoton cewa,a  cikin wani bayani da kwamitin musulmin kasar Amurka ya fitar, ya mayar da kakkausan martani a kan shugaban kasar Faransa Emmanuel macron, dangane da irin matakan takurawa musulmi da yake dauka.

Bayanin ya ce wa’adin kwanaki 15 da Macron ya baiwa musulmi a ranar Laraba da ta gabata kan cewa su yanke shawara kan matsayinsu dangane da dokokin Faransa, wannan abin Allawadai ne.

Bayanin kwamitin ya ce Emmanuel Macron yana kokarin tilasta wa musulmi amincewa da wasu sabbin ka’idoji da dokoki da suka yi hannun riga da koyarwar addininsu, wanda kuma bisa dokokin faransa da ma dokokin na kasa da kasa, Macron ba shi da hakkin yin hakan.

Kwamitin musulmin na Amurka ya ce, Macron yana son mayar da kansa a matsayin wanda zai koya ma musulmi yadda za su yi addininsu, tare da bambance musu abin da yake daidai a cikin addinin muslunci da wanda ba daidai ba a mahangarsa.

Tun bayan zanen batuncin da jaridar kasar Faransa ta yi a kan ma’aiki, muuslmi suka harzuka  aduniya kan yadda macron ya nuna goyon bayansa ga cin zarafin manzon Allah (SAW) da kuma bayar da kariya ga masu yin hakan, tare da kiran musulmin da ba su yarda da cin zarafin manzon Allah ba  amatsayin ‘yan ta’adda, tare da bayyna addinin muslunci a matsayin addinin ta’adanci.

 

3936325

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: