IQNA

Ana Ci Gaba Da Mayar da Martani Kan Kisan Babban Masanin Nukiliya Na Iran Fakhrizadeh

22:52 - November 30, 2020
Lambar Labari: 3485413
Tehran (IQNA) ana ci gaba da mayar da martani dangane da kisan babban masanin ilimin nukiliya na kasar Iran.

A yau kasashe da dama da suka hada da Kuwait, Rasha, Kordestan ta Iraki, Lebanon, Bahrain, Afghanistan, Sin da sauransu sun fitar da bayanai na yin tir da Allawadai da kisan Mohsen Fakhrizadeh,

A nasa bangaren Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Jordan Dhaifullah al-Fayez ya jinjina muhimmancin yin aiki tare a cikin wannan yankin domin rage tashe-tashen hankula da kuma tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Iran dai tana zargin yahudawan sahyuniya da hannu wajen kashe masanin nata farfesa muhsinzadeh a ranar juma’ar da ta gabata.

Ministan harkokin wajen Iran din ta ce da akwai kwararan dalilai da suke nuni da cewa yahudawan sahyuniya suna da hannu a kisan.

Shi kuwa shugaban majalisar koli ta alakar kasashen waje, Kamal Kharrazi ya bayyana cewa; Tabbas Iran za ta mayar da martani mai tsanani akan dukkanin wadanda su ke da hannu a kisan Muhsin Fakhrizadeh.

Sanata Bernie Sanders a majalisar dattawan Amurka ya yi allawadai da kisan masanin fasahar nukliya na kasar Iran Dr Mohsen Fakhrizadeh. Sanders ya bayyana kisan a matsayin wani zagon kasa ga gwamnatin zabebbeb shugaban kasa Joe Biden don hana gwamnatinsa fahimtar juna da kasar Iran.

Kafin haka dai tsohon mai bawa shugaban kasarAmurka shawara kan al-amuran tsaro John Bolton ya yaba da kissan, sannan ya kuma kara da cewa kissan matakin kariya ne ga Isara’ila tun kafin Iran ta kai mata hari.

Amma wani jami’in gwamnatin shugaban Amurka  ya fadawa jaridar Washington Post kan cewa babu ruwan gwamnatin Amurka da kissan na Tehran. Jami’in wanda bai son a bayyana sunansa, ya kara da cewa babu wani kokwanto haramtacciyar kasar Isra’ila ce ta kai harin.

Ministan harkokin wajen Kasar qatar Sheikh Muhammad Abdurrahman ali-Thani ya bayyana kisan gillar da aka yi wa malamin fasahar Nukiliyar na Iran “Muhsin Fakhar Zadeh’ da cewa; Kara ruruta wutar rikici ne.

Ministan harkokin wajen na kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya tattauna ta wayar atrho da takwaransa na Iran, Muhammad Jawad Zarif a jiya Asabar.

Har ila yau ministan harkokin wajen na kasar ya mika sakon gaisuwarsa ga gwamnati da al’ummar Iran, yana mai kara da cewa, matakai irin wadannan ba abin da za su yi illa ruruta wutar rikici a wannan yankin.

Da marecen juma’ar da ta gabata ne dai aka yi wa Muhsin Fakhar Zaden kisan gilla a kusa da birnin Tehran tare da wasu daga cikin masu gadinsa.

 

 

3938418

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha