Shafin jaridar Alkhalij ya bayar da rahoton cewa, a jiya kwamitin fatawa na kasar hadaddiyar daular larabawa ya bayar da fatawar halascin yin amfani da rigakafin cutar corona ga musulmi, ko da kuwa an yi amfani da sanadarin gelatin daga jikin alade.
Sheikh Abdullah Bin Bih shugaban kwamitin fatawa na kasar hadaddiyar daular larabawa ya bayyana cewa, koda an dauki gelatin daga jikin alade, a nan ana maganar hukuncin kubutar da rayuwa ne, saboda haka ya halasta a yi amfani da shi.
Ya cea duk lokacin da aka yi amfani da wani bangare na jikin alade ko wata dabbar da aka haramta domin hada wani magani da zai warkar da mutum daga wata cuta ma illa, to a lokacin abin da ak dauka daga jikin wannan dabbar yana matsayin magani ne, ba abinci ba wanda aka haramta daga jikinta.
Batun yin amfani da sanadarin gelatin daga jikin aladea cikin allurar rigafin corona ya jawo sabani tsakanin malaman musulmi, inda wasu suke ganin rashin halascin yin amfani da ita, yayin da kuma wasu suke kallon hakan a matsayin halas a babin hukunci na biyu.