IQNA

Belgium: Musulmi Sun Yi Lale Marhabin Da Matakin Janye Dokar Hana Saka Hijabi A Jami’oi

21:09 - January 21, 2021
Lambar Labari: 3485576
Tehran (IQNA) Musulmin kasar Belgium sun nuna matukar gamsuwarsu da janye dokar hana saka hijabi a jami’oi da kuam sauran makarantu.

Rahotanni sun bayyana cewa, kungiyoyin musulmi a kasar ta Belgium sun bayyana gamsuwa da irin wannan mataki na soke dokar da ta hana mata muuslmi saka lullubi a cikin jami’oi da makarantun yankunan kudancin kasar.

Babbar kungiyar muuslmi ta kasar ta fitar da bayani a jiya da ke cewa, matakin na nuni ne da gagarumin ci gaba da aka samu, wanda ya baiwa jama’a damar yin aiki da koyarwar addininsu ba tare da wata takura ko take hakkokinsu ba.

A nasu bangaren kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayin kin jinin addinin muslunci a kasar ta Belgium sun nuna bacin ransu matuka da janye wannan doka, wadda wakilansu a majalisa ne suka gabatar da ita kuma aka amince da ita a shekarun baya.

A cikin watan Disamban da ya gabata ne kotun kundin tsarin mulki ta kasar Belgium ta yi watsi da wannan doka, inda ta bayyana ta  amatsayin take hakkokin musulmi, wadanda suke da hannin yin aiki da koyarwar addininsu kamar kowane mutum a kasar, a kan haka kotun ta soke wannan doka.

 

 

 

3948751

 

 

 

 

captcha