IQNA

Shugaba Rauhani: Makaman Kasar Iran Na Kariyar Kai Ne Daga Shishigin Makiya

22:23 - June 15, 2021
Lambar Labari: 3486015
Tehran (IQNA) Shugaba Rauhani na Iran ya jaddada cewa tarin makaman da kasar take mallaka da wadanda take kerawa duk an kariyar kai ne.

Shugaban kasar Iran, Hassan Ruhani, ya bayyana cewa kasarsa ba ta taba niyyar mamaye wata kasa ba, kuma karfafa dakarunta wani salo ne kare kai da kuma tunkarar mamayar makiya.

Shugaba Ruhanin, ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar yaye kallabin wasu sabbin kayan aiki da fasahohi na ma’aikatar tsaron kasar, da suka hada da wasu sabbin jiragen ruwa da aka sanya su aiki.

Shugaban Iran din ya bayyana cewa, yau jamhuriyar musulunci, kasa mai karfi dake tabbatar da tsaron kanta har ma da wasu kasashen yankin makobtanta, inji shi.

A don haka muna tabbatarwa masoyanmu makobtanmu cewa karfin sojinmu ba na amfani da shi akan ku ne ba, a’a na kariya ne da tabbatar da tsaro a tekun Oman, Fasha dama tabbatar da ‘yancinmu da yankinmu a yankin.

Ya ce don tabbatar da wannan tsaron ba mu bukatar makaman kare dangi, kuma ba mu da niyyar mallakar wadannan makaman, saboda wannan fatawa ce ta jagora.

Kasashen yammacin duniya dai suna nuna fargaba dangane da makaman da Iran take mallaka musamman ma makamai masu linzami daga cikinsu, wadanda take kerawa a cikin gida ta hanyar yin amfani da fasahar zamani mai zurfi, wanda hakan yasa kasashen yammacin ba su san yadda aka kera makaman ba, balanta su san yadda za su kera wadanda za su kalubalance su.

3977393

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :