IQNA

21:00 - July 23, 2021
Lambar Labari: 3486132
Tehran (IQNA) kungiyar Hizbullah ta mayar da kakkusar martani dangane da hare-haren da Isra’ila take kaddamarwa kan kasar Syria.

Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ta mayar da kakkusar martani dangane da hare-haren da Isra’ila take kaddamarwa kan kasar Syria, da kuma yadda duniya ta yi gum da bakinta kan hakan.

Bayanin na kungiyar Hizbullah ya ce, Isra’ila tana yin amfani da damar da ta samu wajen aikata abin da ta ga dama, ba tare da wani ko wata kasa ta isa ta ce uffan ba, saboda goyon bayan da take da shi daga gwamnatin Amurka, da hakan ya hada har da kai hare-hare a kan kasashen da ta ga dama.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, Isra’ila ta yi amfani da sararin samaniyar kasar Lebanon wajen kai wa kasar Syria hari a jiya Alhamis, amma har yanzu babu wani martani daga bangarori na kasa da kasa kan hakan.

A jiya Alhamis ne dai Isra’ila ta kai hare-hare a yankin Qusair da ke cikin gundumar Homs a kasar Syria, inda ta harba makamai masu linzami a kan wasu wurare na sojin kasar, amma makaman kariya na rundunar sojin kasar at Syria sun kakkabo dukkanin makaman da Isra’ila ta harba.

3985807

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: