Muhammad Mukhtar Juma'a minista mai kula da harkokin addini na kasar Masar ya sanar da cewa, an kara wasu bangarori da rassa guda biyua cikin gasar kur'ani mai tsarki ta duniya ta kasar Masar.
Ministan ya bbayana hakan ne yau a lokacin da yake ganawa da limaman masallatai na kasar, inda ya ce an kara bangaren hardar dukkanin kur'ani tare da tafsirin ayoyinsa.
Ya ce wannan zai kebanci malamai ne wadanda suke gudanar da ayyuka na wa'azi 'yan kasar Masar kawai, ba zai shafi baki da za su halarci gasar ba.
Haka nan kuma ya kara da cewa, kara wannan bangaren zai taimaka ma masu wa'azi da za su shiga gasar su kara zama cikin shiri, kuma su samu cikakkiyar masaniya kan tafsirin ayoyin kur'ani sahihin tafsiri.
Ministan ya ce an bayar da wa'adi daga nan zuwa 15 ga watan Oktoban wannan shekara dukkanin wadanada za su halarci su tabbatar ad sun kammala yin rijistar sunayensu, domin kuwa za a gudanar da gasar nea cikin watan Disamban karshen wannan shekara.