IQNA

Jami'an Tsaro A Iraki Sun Fara Daukar Kwararan matakan Tsaro Domin Tarukan Arba'in

22:17 - September 05, 2021
Lambar Labari: 3486274
Tehran (IQNA) jami'an tsaro a kasar Iraki sun fara daukar kwararan matakan tsaro domin tarukan Arba'in da za a gudanar.

Kamfanin dillancin labaran Mawazin News ya bayar da rahoton cewa, an fara daukar tsauraran matakan tsaro a kasar Iraki domin tarukan arba'in da za a gudanar.

Rahoton ya ce, a yankin Bagdad jami'an tsaro suna sintiri a cikin gari da kuma cikin dazuzzuka domin tabbatar da cewa babu wasu 'yan ta'adda da za su kawo barazana ta tsaroa  yayin gudanar da tarukan Arba'in.

Baya ga haka kuam sauran yankuna musammanma biranan Karbala da kuma Najaf, tun bayan kammala taruka ashura har yanzu jami'an tsaro suna nan cikin shirin ko ta kwana.

Daga cikin matakan da ake dauka dai kula da layuka na wutar lantarki da kuma layukan butun gas, kamar yadda kuam ake sanya ido a kan dukkanin kai koma na jama'a.

Sannan kuma an kafa kamarori masu daukar hotunan bidiyo a dukkanin yankuna da titina na mayna birane musamman Karbala da Najaf.

 

 

3995311

 

 

 

 

captcha