Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Muhamamd Al-na'is dattijo ne dan shekaru 70 da haihuwa, wanda ya hardace kur'ani shekaru biyar da suka gabata a cikin tsufansa.
Ya ce tun a shekarun baya ne 'yan ta'adda da suka addabe su a kauyensu, hakan yasa ala tilas suka yi gudun hijira suka kaurace ma kauyen.
Muhammad ya ce,a lokacin gudun hijirar ne ya samu matsalar gani sakamakon irin makaman da 'yan ta'adda suka rika harbawa a kan jama'a musamamn wadanda basu goyon bayansu.
Sakamakon haka ne kuma ya rika amfani da rikoda mai amfani da kaset wajen sauraren karatun kur'ani, kuma a cikin wadanann shekaru kasa da biyar ne ya hardace kur'ani mai tsarki baki daya.
Wannan dattijo dai ana bayyana shi da cewa yana da kaifin basira wajen rike komai a kwakwalwarsa, inda ya hardace suanayen dukaknin shugabannin kasashen duniya, da kuma sunayen manyan tekuna na duniya.