IQNA

Cikar Shekaru 20 Da Kai Harin 11 Ga Watan Satumba A Kasar Amurka

22:10 - September 11, 2021
Lambar Labari: 3486297
Tehran (IQNA) a yau ne aka cika shekaru ashirin da kai harin 11 ga watan satumba a kasar Amurka

A ranar Talata 11 ga Satumban 2001, ne wasu masu alaka da kungiyar al- Ka’ida su 19 suka kwace jiragen sama guda 4 tare da kai hare-haren kunar bakin wake a Amurka kan tagwayen gine gine na Cibiyar kasuwanci ta Duniya da ke birnin New York, da ma’aikatar tsaro ta Pentagon da ke Washington, yayin na fado, a jihar Pennsylvania.

Kusan mutane 3,000 suka mutu yayin harin wanda ya kasance mani muni a tarihin Amurka.

Shugaban Amurka Joe Biden, sabanin shugabanin da suka gabace shi, ya fitar da wani faifan bidiyo maimakon yin jawabi yayin bikin zagayowar ranar inda ya bukaci Amurkawa dasu hada kansu, wanda shi ne karfin kasar inji shi.

Kafin hakan dai, Mista Biden ya ba da umarnin sakin wasu bayanan sirri dangane da binciken gwamnati kan harin na ranar 11 ga watan satumban 2001.

 

3996388

 

captcha