IQNA

Malaman Kasar Bahrain Sun Yi Allawadai Da Ziyarar Ministan Isra'ila A Kasarsu

19:45 - October 02, 2021
Lambar Labari: 3486373
Tehran (IQNA) daruruwan malaman kasar Bahrain ne suka yi tir da ziyarar farko da ministan harkokin wajen Isra’ila ya kai a kasarsu.

Shafin Alwefaq ya bayar da rahoton cewa, fiye da malaman kasar Bahrain dari biyu da hamsin ne suka yi tir da kuma kakkausar suka kan ziyarar farko da ministan harkokin wajen Isra’ila ya kai a kasar da ke yankin tekun Fasha, tun bayan da gwamnatoci biyu suka kulla alaka a bara.

Bayanin malaman na Bahrain na hadin gwiwa ya ce: "Muna Allah wadai da kasancewar ministan harkokin waje na yahudawan sahayoniya a Bahrain, kuma muna sabunta ƙin amincewa da duk wani tsari na daidaitawa tare da gwamnatin ‘yan mamaya,  gami da buɗe ofishin jakadanci da ofishin kasuwanci a birnin Manama.”

Bayanin ya kara da cewa: "Muna kuma jaddada goyon bayanmu ga al'ummar Falasdinu, wadanda suka yi sadaukarwa wajen kare kasarsu da al’ummarsu da kuma wurare masu tsarki da ke Falastinu da suka hada da masallacin Quds mai alfarma, wanda wasu daga cikinsu suka yi shahada a kan wannan tafarki.”

Ministan harkokin wajen Isra’ila Yair Lapid ya isa filin jirgin saman Manama a ranar Alhamis, wanda shi ne babban jami’in Isra’ila da ya ziyarci kasar da ke yankin Tekun Fasha tun lokacin da Isra’ila da Bahrain suka kulla kawance a bara.

Ya kuam gana da Sarki Hamad bin Isa Al Khalifah da Yarima mai jiran gado da Firaminista Salman bin Hamad Al Khalifah.

A ranar Juma'a, gungun matasa sun taru a wajen ofishin diflomasiyya tare da daga tutocin Falasdinu domin yin Allah wadai da matakin gwamnatin Al Khalifah, na daidaita alakar da ke tsakaninta da Isra'ila, tare da bayyana goyon bayansu ga al'ummar Falasdinu.

 

4001672

 

captcha