IQNA

Kungiyoyin Falastinawa Sun Mayar Da Martani Dangane Da Ziyarar Ministan Isra'ila A Bahrain

22:48 - October 02, 2021
Lambar Labari: 3486377
Tehran (IQNA) kungiyoyin Falastinawa sun mayar da martani dangane da ziyarar ministan Isra'ila a kasar Bahrain

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, dangane da ziyarar da  ministan harkokin wajen Isra'ila ya kai a kasar Bahrain kungiyoyin Falastinawa sun mayar da martani.

A cikin bayanan da suka fitar na hadin gwiwa, kungiyoyin falastinawa daban-daban sun yi Allawadai da kakausar murya dangane da ziyarar da ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan Isra'ila ya kai a kasar Bahrain.

Bayanin ya ce, irin wannan mataki na gwamnatin Bahrain, yana a matsayin cin amana ne ga al'ummar falastinu da ma sauran al'ummar musulmi, ta yadda gwamnatin kasar ta mika kai ga yahudawa kai tsaye ba tare da la'akari da abin da take aikatawa a kan Falastinawa da sauran musulmi na yankin ba.

Sannan kuma bude ofishin jakadancin Isra'ila a Bahrain, yana a matsayin halasta dukkanin abin da take yi ne na kisan musulmi a Falastinu da mamaye musu kasa, da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki da ke Falastinu da Isra'ila ke yi, da hakan ya hada da masallacin Quds, alkiblar musulmi ta farko.

 

001614

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha