IQNA

Japan Na Kara Fadada Ayyukan Bude Ido Na Musulunci

20:44 - October 03, 2021
Lambar Labari: 3486379
Tehran (IQNA) masallacin Shizuoka na daga cikin muhimman wurare na musulmi a kasar Japan da ke jan hankulan masu yawon bude ido.

Duk da cewa addinin muslunci yana daga cikin addinai masu mabiya 'yan tsiraru a kasar Japan, amma kuma a lokaci ana baiwa addinin musluci muhimmanci matsayi na musamman a kasar.

Ma'aikatar bunkasa al'adu da kula da ayyukan bude a kasar Japan, ta sanya masallacin Shizuoka a matsayin daya daga cikin muhimamn wurare a kasar, wadanda masu zuwa yawon bude ido za su iya ziyartar wurin.

Wanann masallacin da ake kira da koren masallaci ko kuma Green Mosque, yana daga cikin wurare na musulmi wanda aka yi amfani da fasaha ta musamman wajen gininsa da ke daukar hankula matuka.

Akasarin msuulmin da suke rayuwa a kasar Japan dai sun zo ne daga kasashe daban-daban, musamman kasashen larabawa da kuam kasashen gabashin Asia, gami da kadan daga cikin mutanen kasar wadanda suka karbi addinin muslunci.

Musulmi suna rayuwa a cikin 'yanci na gudanar da dukkanin harkokinsu na addini ba tare da wata tsangwama ko cin zarafi, ko kuma nuna musu banbanci ba.

 

4000042

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: musulmi kasar Japan
captcha