IQNA

An Fara Gudanar Da Shirye-Shiryen Tarukan Makon Hadin Kai A Iran

18:12 - October 16, 2021
Lambar Labari: 3486432
Tehran (IQNA) An fara gudanar da shirye-shiryen tarukan makon hadin kai tsakanin al’ummar musulmi da aka saba yi a kowace shekara.

Hukumomi  kasar Iran sun sanar da cewa, yanzu haka an fara gudanar da shirin taron makon hadin kai na musulmin duniya, wanda aka saba gudanarwa a kowace sheakara, tare da halartar masana da malamai da jami’ai daga kasashen musulmi daban-daban.

Wannan dai shi ne karo na talatin da biyar da za a gudanar da wanna taro, tun bayan da marigayi Imam Khomeini ya ayyana ranar sha biyu zuwa sha tara ga watan Rabi’ul Awwal a wato makon haihuwar manzon Allah (SAW) da ya zama makon hadin kan musulmi na duniya baki daya.

Wannan dai yana zuwa ne sakamakon irin kalu balen da ke fuskantar duniyar musulmi ne, inda musulmi suka shagala da kawukansu, suka manta da abin da yake a gabansu na manyan kalu bale daga makiyansu, duk kuwa da cewa shagaltar da musulmi da junansu shi kansa yana daga cikin abubuwan da aka shirya musu, kuma da dama daga cikinsu ba su fahimci hakan ba.

Marigayi Imam Khomeini ya yi kokarin nuna wa duniyar musulmi cewa, abin da ya hada musulmi ya fi abin da ya raba su girma, domin kuwa imani da Allah da manzon Allah da sakon da ya zo da shi daga Allah su ne abin da suka hada musulmi, wanda kuma shi ne tushe a cikin addini, duk sauran abubuwan rassa ne, wanda za a iya samun sabinin fahimta akansu, amma babu sabanin fahimta kan imani da Allah da manzonsa da kur’ani a tsakanin dukkanin musulmi.

Wannan ne babban dalilin da yasa marigayin ya sanya wannan mako ya zama makon hada kan musulmi, domin ko da wata fahimta ko ra’ayi ya raba su, to manzon Allah ya hada su, a kan haka makon da ake murnar zagayo da lokacin haihuwarsa, shi ne yafi dacewa da makon hadin kan al’ummar manzon Allah.

 

4005214

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha