IQNA

Musulmin Uganda Sun Koka Kan Cin Zarafin Dalibai Mata Musulmi A Jami'a

22:08 - December 07, 2021
Lambar Labari: 3486656
Tehran (IQNA) Dalibai musulmi a wata jami'a a kasar Uganda sun bukaci jami'an 'yan sanda mata da su duba dalibai mata maimakon jami'an tsaro maza.

Shafin yada labarai na Obsever ya bayar da rahoton cewa, Fitar da wani faifan bidiyo na wani jami’in ‘yan sanda ya tilasta wa dalibai mata musulmi cire hijabi, ya sa daliban jami’ar Kymbogo suka yi kira da a girke jami’an 'yan sanda mata a wuraren bincike cikin jami'ar.

Sheikh Bakhit Koko, Sakataren Ilimi na Majalisar Musulmi ta Uganda (UMSC), ya bayyana matakin da jami’in ya dauka a matsayin cin zarafin ‘yancin addini, wanda aka tanada a cikin kundin tsarin mulkin Uganda, yana mai cewa hakan na zubar da mutuncin dalibai mata musulmi.
 
Tun da farko dai an samu irin wannan lamari a jami'ar, inda aka hana wata daliba shiga jami'ar saboda ta ki cire hijabi.
 
Tun bayan harin ta'addancin da wasu masu da'awar jihadi suka kai a birnin Kampala a 'yan makonnin da suka gabata, mahukuntan kasar Uganda suka fara dora karan tsana a kan musulmin kasar, lamarin da ke ci gaba da shan suka daga kungiyoyin musulmi na ciki da wajen Uganda, da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama.
 
Akwai kimanin musulmi miliyan 9 daga cikin mutane miliyan 45 na kasar Uganda da ke gabashin nahiyar Afirka.
 

 

4018869

 

captcha