IQNA

An Girmama Mutumin Da Ya Rubuta Kur'ani Mafi Tsawo Da Hannunsa

22:29 - December 08, 2021
Lambar Labari: 3486660
Tehran (IQNA) Shugaban Jami’ar Tanta da ke Masar ya yi maraba da Saad Hashish, wanda ya rubuta kwafin kur'ani mafi tsawo da hannunsa.

A rahoton da shafin Al-Bayan ya bayar, Saad Hashish, marubucin Mus'haf mafi tsawo a duniya, ya gana da Mahmoud Zaki, shugaban jami'ar Tanta da ke Masar a jiya.

“Ni ba malami ba ne, amma ina alfahari da na iya koyon karatu da rubutu da kaina,” in ji Hashish, yayin da yake magana kan yadda aka haife shi a wani kauye da ke lardin yammacin Masar.

 

https://iqna.ir/fa/news/4019089

Abubuwan Da Ya Shafa: rubutu da karatu ، marubucin ، mafi tsawo ، a duniya ، koyon karatu ، kauye
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha