IQNA

Masallacin Paris Ya Bayar Da Kyautar Kur'ani Ga Shugaban Kasar Aljeriya

23:32 - December 11, 2021
Lambar Labari: 3486672
Tehran (IQNA) Kwamitin Masallacin Paris ya bayar da kyautar kwafin kur'ani mai tsarki a ga shugaban kasar Aljeriya a birnin Algiers, babban birnin kasar.

Shafin jaridar Al-nahar ya bayar da rahoton cewa, An yi ganawar ne a ranar Alhamis 9 ga watan Disamba, inda Shamsuddin Hafiz (Hafiz), mai kula da  masallacin Paris, ya gabatar da kwafin kur'ani na Faransanci na Hamza Abu Bakr ga shugaban kasar Aljeriya Abdel Majid Taboun. .

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar Aljeriya ta fitar ta ce taron ya gudana ne bisa bukatar Shamsuddin Hafiz, inda shugaban kasar Aljeriya ya jaddada cewa masallacin birnin Paris wani tsohon wuri ne na ibada kuma na tarihi.
 
Tebun ya kuma ba da shawarar cewa masallacin ya ci gaba da kokarin yada matsakaicin ra'ayi da fuskantar tsatsauran ra'ayi, sannan ya ci gaba da bin salo na daidaita kan musulmi da kuma karfafa zaman lafiya a tsakaninsu da sauran al'ummomi.
 
Daraktan ofishin shugaban kasar Aljeriya Seyed Abdul Aziz Khalaf, da ministan harkokin addini Seyed Yousef Belmehdi, sun halarci ganawar, a lokacin da aka mika wa shugaban na Aljeriya wannan kyauta.
اهدای قرآن از سوی تولیت مسجد پاریس به رئیس‌جمهور الجزایر
 
 
 
 
Abubuwan Da Ya Shafa: masallaci ، harkokin addini ، karfafa zaman lafiya ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha