IQNA

22:56 - January 15, 2022
Lambar Labari: 3486824
Tehran (IQNA) Wata kungiyar Falasdinu ta yi kira ga kungiyar agaji ta Red Cross da ta binciki lafiyar fursunonin Falastinawa da ke kurkukun Isra'ila sakamakon yaduwar Corona.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, Hukumar 'Yancin Falasdinu mai alaka da kwamitin kare hakkin  Fursunoni da 'Yancin Falasdinu ya yi kira ga kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa da ta ziyarci fursunonin falastinawa mata a gidan yarin Damon da ke arewacin Falasdinu domin tantance lafiyarsu.

An gabatar da bukatar ne a cikin wata sanarwa da kungiyar agaji ta Red Cross ta fitar, bayan da aka samu karuwar fursunonin mata da ke dauke da kwayar cutar Corona a gidan yarin.

Kungiyar ta ce adadin fursunonin mata da suka kamu da cutar ta Corona ya kai bakwai, lamarin da ke kara sanya damuwa da fargabar dangane da halin da suke ciki.

Kwamitin ya dora wa hukumar gidan yari cikakken alhakin rayuwar mata fursunoni da ake tsare da su.

A ranar alhamis, kungiyar fursunoni ta Falasdinu (mai zaman kanta) ta ce a cikin wata sanarwa cewa; adadin fursunonin da suka kamu da cutar ta Corona tun daga watan Afrilun 2021 ya karu zuwa 410.

Wannan rahoto ya biyo bayan sanarwar rashin lafiyar Hisham Abu Hawash ne, wani fursuna Bafalasdine wanda ya kwashe tsawon kwanaki 141 yana yajin cin abinci.

Ya zuwa karshen watan Disamba, adadin fursunonin Falasdinawa da wadanda ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila ya kai 4,600, da suka hada da ma’aikata 500, da fursunoni mata 34, da kuma yara kanana 160.

 

4028536

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kungiyar agaji ta Red Cross ، sanarwa ، arewacin Falasdinu ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: