IQNA

A Yau Ne Shugabanin Iran Da Rasha Za Su Gana A Birnin Moscow

16:39 - January 19, 2022
Lambar Labari: 3486840
Tehran (IQNA) A wani lokaci yau Laraba ne shugaban kasar Iran, Ibrahim Ra’isi, zai gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin.

Shugabannin Iran da Rasha zasu gana ne a birnin Moscow, yayin ziyarar aiki da shugaban kasar ta Iran ya kai a Rasha, wacce ita irinta ta farko tun bayan da hau kan karagar mulki.

Gabanin ziyarar tasa shugaban kasar ta Iran, ya bayyana cewa alaka tsakanin Moscow da Tehran, za ta karfafa zaman lafiya a yankin da kuma kawo karshen shishigi na kasashen ketare.

Kasashen biyu kuma zau karfafa alaka tsakaninsu ta fuskar diflomatisyya da kuma makwabtaka da kuma batutuwan da suka shafi yankin, kamar yadda kamfanin dilancin labaren IRNA, ya rawaito.

Kasashen Iran da Rasha dai na da dadadiyar alaka a tsakaninsu, bayan kasancewarsu mambobi a kungiyoyi na tattalin arziki da kuma na yankin da dama.

Yayin ziyarar bangarorin zasu tabo batutuwan da suka shafi alaka, siyasa, tattalin arziki, makamashi, ciniki, harkokin zurga zurga sama da kuma na sararin samaniya.

 

 

4029685

 

 

captcha