A daidai lokacin da zaben shugaban kasa ke karatowa a kasar Faransa 'yan siyasa sun mayar da nuna kyama ga addinin muslunci a matsayin abin kamfe na siyasa.
Tun bayan da 'yan siyasa suka fara kamfen na neman kuri'a a zaben shugaban kasa da za a gudanar a kasar, nuna kyama ga musulunci ya zama abin yin kamfe, inda kowane dan takara da yake son ya burge masu yamar musulunci ko neman samun kuriunsu sai ya dira kan musulunci da musulmi.
Jam'iyyar Emmanuel Macron mai mulki na daya daga cikin jam'iyyun da suka dauki wanann salon, kuma wannan ya fara ne tun a shekarar da ta gabata.
Duk da cewa a halin yanzu a kasar Faransa musulmi su ne na biyu bayan mabiya addinin kirista, amma har yanzu suna fuskantar ayyukan nuna musu wariya a hukumancea kasar, wadda take ikirarin bin tafarkin demokradiyya da kuma hakkokin addini.