IQNA

Kungiyar malaman musulmin Iraqi ta bukaci a kori Mossad daga yankin Kurdistan

22:03 - March 18, 2022
Lambar Labari: 3487070
Tehran (IQNA) Kungiyar malaman musulmi ta lardin Diyala da ke gabashin kasar Iraki ta aike da sako ga Massoud Barzani, shugaban jam'iyyar Kurdistan Democratic Party ta Iraki, inda ta bukace shi da ya kori 'yan kungiyar Mossad daga yankin Kurdawa nan take a yau 17 ga watan Maris.

A cikin sakon, Jabbar al-Ma'mouri, shugaban kungiyar hadin kan malaman musulmi a lardin Diyala na kasar Iraki, ya yi kira ga Massoud Barzani da ya kori kungiyar Mossad daga yankin Kurdistan na Iraki ba tare da wani sharadi ba, kamar yadda shafin yada labarai na Al-Ma'loumeh na kasar Iraki ya bayyana.

Ya jaddada cewa karbar Mossad na barazana ga zaman lafiya da tsaro a lardin Diyala da kewaye.

Al-Ma'mouri ya ce lokaci ya yi da jami'an yankin Kurdawa na Iraki za su aika da sakon tabbatarwa ga 'yan Iraki da kasashen da ke makwabtaka da kasar cewa kasancewar Mossad jan layi ne, kuma za a kore su nan take.

Ya kara da cewa: Kundin tsarin mulkin kasar ya haramta duk wata kungiya da ke da hadari ga zaman lafiya da tsaron kasar, ballantana Mossad, wanda a matsayinsa na mugun dan aike yana barazana ga hadin kan kasa.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4043860

captcha